Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon 2023 na daliban da suka zana jarabawar tare da samun kashi 61.6 na wadanda suka samu Ingilishi da Lissafi.
Da yake fitar da sakamakon na NECO a ranar Talata, magatakardar hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce jimillar dalibai 1,196,985 ne suka zauna zana jarabawar.
Ya ce daga cikin jimillar dalibai da suka zauna jarabawar, 737,308 sun samu nasara da kiredit biyar zuwa sama da suka hada da harshen Ingilishi da lissafi, wanda ke wakiltar kashi 61.60 cikin 100 na dalibai 1,196,985 kuma sun cancanci shiga jami’a.
A wani labarin na daban dan wasan gaban Super Eagles na Nijeriya Victor Boniface na ci gaba da haskakawa a kungiyarsa ta Bayer Leverkusen da ke buga gasar Bundesliga ta kasar Jamus.
Dan wasan mai shekaru 22 zai fafata da dan wasan tsakiya na RB Leipzig Xavi Simons da kuma dan wasan gaba na Hoffenheim Maximilian akan kyautar gwarzon dan wasan Bundesliga na watan Satumba.
Boniface ya zura kwallaye biyu kuma ya taimaka an zura kwallaye uku a wasanni hudu da ya buga wa Bayer Leverkusen a watan Satumba.
Boniface yana jin daɗin rayuwa a babbar gasar Jamus bayan zuwansa daga kungiyar kwallon ƙafa ta Belgian Pro League Union St. Gilloise.
Source LEADERSHIPHAUSA