Shugabannin jam’iyyar PDP na kwamitin NEC sun yi magana kan yadda za su tafiyar da gwamnonin da ke fushi a jam’iyyar, irinsu Samuel Ortom, Nyesom Wike da saura.
Babban jigon jam’iyyar, Bode George, ya ce ya kamata PDP ta yi taka tsantsan kuma ta yi hakuri da su.
A ganin George, ko PDP tana so ko bata so, Wike da mutanensa za su yi duk abin da suke so idan Iyorchia Ayu ya ki yin murabus.
Mambobin kwamitin zartarwa (NEC) na jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) sun ce za su cigaba neman yin sulhu da gwamnonin da suke ganin an zalunce su.
Bode George ya yi kira a yi taka tsantsan
A bangarensa, tsohon ciyaman din kwamitin amintattu na jam’iyyar, Cif Bode George, ya shaida wa Punch cewa dole jam’iyyar ta yi amfani da hikima tare da taka tsantsan wurin tattaunawa da wadanda suke ganin an zalunce su.
A yayin da ya ke kira ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya kasance mai kishin kasa a maganganunsa, George ya kuma bukaci Iyorchia Ayu ya yi amfani da hularsa na tunani a yayin warware matsalolin da ke adabar jam’iyyar.
A ganin George, idan jam’iyyar na shirin hukunta wasu mutane, ba yanzu ne lokacin da ya dace a yi hakan ba. Kalamansa: “Ko da jam’iyyar na son yin hakan (hukunta su), ba yanzu ne lokacin da ya dace ba.
A matsayin dattijon jam’iyya, idan Atiku ya dage cewa ba zai saurari kowa ba kuma Ayu ya cigaba da nuna fushinsa a ko ina, duk abin da kowa ke son yi, za su yi.
Wannan gwamnonin ba kanwan lasa bane, kuma ya kamata Atiku ya san hakan.”
A bangare guda, Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers, ya ce jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, za ta ci zabe a jiharsa a 2023. Amma, gwamnan ya ware zaben shugaban kasa ya kore yiwuwar nasarar Atiku Abubakar a jihar, sai dai idan ya yi abin da ya dace, Vanguard ta rahoto.
Wike ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da sabbin ofisoshin sadarwa a gunduma 319 da mazabu 32 a Port Harcourt, babban birnin jihar.
Source:legithausang