Duk surutan da ake yi a kan sababbin Nairori, Muhammad Ali Ndume ya ce bai taba rike su ba.
Sau daya kurum Sanata Muhammad Ali Ndume ya ga sabuwar N1000, kuma tun a shekarar bara.
‘Dan majalisar yana cikin masu kira ga bankin CBN a tsawaita wa’adin daina karbar tsohon kudi.
Nan da ‘yan kwanaki za a daina amfani da tsofaffin takardun N200, N500 da N1000 a Najeriya, amma ana yawan kukan karancin sababbin kudi.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa daga cikin masu kukan har da Muhammad Ali Ndume, wanda ya ce har yanzu bai ci karo da sababbin takardun ba.
Duk da yana cikin manyan ‘yan majalisar dattawan kasar nan, Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce bai rike sabuwar N1000 da sauran kudin da aka buga ba.
‘Dan siyasar yake cewa idan aka tafi a haka, mafi yawan ‘yan Najeriya za su gamu da cikas a dalilin matakin nan da babban bankin kasar nan ya dauka.
Ba a komai ake kawo siyasa ba ‘Dan majalisar Kudancin jihar Bornon ya shaidawa Vanguard haka, sannan ya kara da sukar mutanen da ke siyasantar da canjin kudin da CBN ya yi.
Sanatan yake cewa ba a kowane tsari ko manufa da aka fito da shi za a rika biyewa siyasa ba.
Lokacin nan ba zai isa ba – Ndume
Da aka tambayi Ndume ra’ayinsa a game da wa’adin da aka bada na 31 na Junairun 2023, sai ya nuna cewa bai tunanin lokacin da aka kayyade zai isa.
“Lokacin ba zai yiwu ba, shiyasa na kawo magana a zauren majalisar dattawa, mu na rokon CBN ya tsawauta wa’adin domin a iya karbar tsofaffin kudi.
CBN ne ya bada sanarwar tsawaita wa’adin, amma har yanzu ba su yi.
Abin takaicin shi ne har zuwa yanzu babu sababbin kudin nan. – Mohammed Ali Ndume
Kamar yadda Ndume yake fada, su na so ne a kara tsawon wa’adin zuwa karshen watan Yuni. Ndume ya taba ganin sababbin kudi?
“A matsayin Sanata, ban taba gani ba, sau daya kurum na taba ganin sabon kudin a Disamba, da na kawo maganar ne wani abokin aikina ya nuna mani N1000.
Tun lokacin na ke cire kudi a banki, har yanzu ba a taba ba ni sabon kudi ba. Ko a ranar Juma’a na zari kudi a banki, kuma tsofaffin takardun nan aka ba ni.
” Man fetur zai koma N800-N900? Ku na da labari babu mamaki man da ake saye tsakanin N180 zuwa N300 ya dawo sama da N800 a shekarar nan, farashin zai iya komawa kamar na dizil.
Wani Sakataren kungiyar IPMAN, Mohammed Shuaibu ya hango karin kusan 400% idan aka cire tallafin fetur kamar yada gwamnatin nan ta ke magana.
Source:LegitHausa