Mai shari’a H. Mu’azu na babbar kotun birnin tarayya ya bayar da umarnin wucin gadi na hana Sanata Mohammed Ali Ndume daukar duk wani mataki na kai hari, ko muzgunawa, ko kuma barazana ga wani malamin Addinin Musulunci a Abuja, Imam Ibrahim Lawal Osama.
Kotun ta ba da umarnin ne a cikin doka mai Lamba FCT/HC/CV/7043/2023 MOTION NO: FCT/HC/M/12227/2023, sakamakon bukatar da lauyan masu shigar da kara A.L. Likko, Esq, da D.M. Yakubu Duks, Esq suka yi.
An dai zargi Sanata Ndume mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu da bayar da umarnin kai wa Imam Osama hari, a lokacin da ake gudanar da taron addu’o’i na musamman a masallacin Apo Legislative Quarters Zone (B) da ke Abuja.
A cikin takardar kotun da wani lauyan Nijeriya ya gani, kotun ta bayar da umarnin kamar haka:
“An ba da iznin wucin gadi da ke hana wadanda ake kara, ko dai su kansu, ko jami’ansu, ko wakilansu, da aka ba su, ko na sirri, ko duk wani wanda ya yi aiki a madadinsu ko ya samu izini daga gare su daga sake kamawa ko kuma ci gaba da tsare Imam Lawal Ibrahim Osama, ko yin duk wani aiki da zai keta hakkinshi, ‘yancin kai, hakkin mutunta dan adam har zuwa lokacin sauraren ra’ayi da kudurin da aka shigar a gaban wannan Kotun Mai Girma.
“An ba da umarnin hana masu amsa, ko da kansu, ba da izini. wakilai, kebabbu, ko duk wanda ke da niyyar yin aiki a madadinsu daga keta ko kara keta hakkinsa.
Mai kara kamar yadda sashe na 33, 34 (1) ya tabbatar 35 (1) & (4), 37, 39, 43, da 45 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara).
“An ba da umarnin hana wadanda ake kara da kansu, ko aka ba su, ko na sirri, ko wakilai ko duk wanda ke da niyyar yin aiki a madadinsu daga keta ko kara shiga hakkin wanda ke kara ko kuma a kan sharuddan da wannan Kotun Mai Girma ta ga ya dace a cikin kotun yanayi, har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin wannan zama.
An dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 17 ga watan Agusta, 2023, domin sauraren wata muhimmiyar bukata.
Majiya mai tushe ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yayin wani taron addu’o’i na musamman ga al’ummar kasar da aka gudanar a masallacin Apo, inda Hafizai da dama suka karanta Alkur’ani mai girma domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.”
Ana zargin Sanata Ndume da shiga masallacin ne a cikin gungun ’yan daba, kuma ya bukaci da a dakatar da addu’ar, sannan a kulle masallacin.
Hatsaniya ta barke sannan aka katse gudanar da taron karatun.
Imam Ibrahim wanda ya jagoranci addu’ar ya bukaci Sanatan da ya ci gaba da maraba da kuma girmama alfarmar wurin ibada.
Maimakon ya saurari rokon malamin, Sanatan ya yi zargin cewa ya fusata kuma ya umarci ’yan kungiyarsa su kai masa farmaki a gaban masu ibadar da suka firgita.
Malamin ya ci gaba da cewa Sanata Ndume tare da rakiyar ’yan uwansa sun yi masa mummunar wulakanci da suka hada da naushi, harbin bindiga, da kuma kalamai masu cike da barazana rikicin ya kaure ne a dai-dai lokacin da wasu masu ibada suka shiga tsakani suka yi nasarar hana Sanatan da ‘yan tawagarsa.
Malamin ya samu munanan raunuka inda nan take aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
A halin yanzu yana cikin ƙoshin lafiya amma dai tarzomar ta haddasa mashi rauni.
Nan take malamin ya kai karar lamarin a ofishin ‘yan sanda mafi kusa, kuma Sanata Ndume ya ki amsa gayyatar ‘yan sandan.
Source: LEADERSHIPHAUSA