Sanata Ali Ndume ya yi Alla-wadai da Ministan Kwadago da sauran masu fafatawa da Malaman ASUU.
Ndume ya ce yan majalisan da basu aikin komai ana biyansu makudan albashi amma a hana Malamai.
Bayan watanni takwas da yajin aiki, Malaman ASUU sun samu rabin albashin watan Oktoba kadai.
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu ya bukaci gwamnatin tarayya ta rage albashin yan majalisa da biyu don biyan kudin albashin Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU.
Ndume ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Maiduguri, birnin jihar Borno, rahoton TheCable. Sanatan ya shawarci gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaske ba kalaman baki ba.
Yace: “Ko da za’a rage albashin yan majalisan tarayya ne ko a su bi bashi, ko a rage albashinsu don biyan Malaman ASUU. Ayi hakan don amfanin daukacin yan Najeriya.”
“Sau biyu kadai muke zama a mako kuma ana biyanmu makudan kudade. Ma’aikatan gwamnati da basu je aiki ba tsawon lokacin Korona an biyasu albashi da alawus dinsu.”
“Me zai hana gwamnatin tarayya ta biya Malaman jami’a da suka shiga yajin aiki?
A doka ai hakkinsu suke karewa”
“Maganar gaskiya itace mu yan majalisa babu aikin da muke yi; saboda haka a raba albashinmu biyu a biya ASUU.”
“Mun yi kasafin N20.5 trillion wa 2023. Ban ga dalilin da zai hana gwamnati kasafin 1tr don magance matsalar ASUU ba.”
“Yawancin wadanda ke zaman magance matsalar ‘yayansu ba su karatu a jami’o’in gwamnati. Ko ni ‘yayana a kasar waje suke karatu, yawancin yan siyasa ma haka ne.”
Gwamnatin tarayya ta raina mana wayo, ASUU Shugaban Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya, ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya dira kan gwamnatin tarayya kan biyan albashin rabin watan Oktoban da ta yiwa mambobinta.
Gwamnatin tarayyan tayi bayanin cewa ta biya malaman albashi ne bisa ranakun da sukayi aiki, saboda ba zata biyasu kudin aikn da basu yi ba.
Shugaban ASUU a martaninsa yace mambobinsu ba ma’aikatan wucin-gadi bane kuma bai kamata a dinga yi musu wulakanci tamkar wasu leburori ba.
Ya kara da cewa ko kadan ba zasu koma yajin aiki ba.
SOURCE:LEGITHAUUSA