NDLEA ta ce ta kama ‘sarauniyar ƙwaya’ a Jihar Taraba.
Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta kama wata mace da ta kira “Sarauniyar Ƙwaya” a Jihar Taraba da ke tsakiyar ƙasar sakamakon zarginta da ta’ammali da tabar wiwi.
Sanarwar da NDLEA ta fitar a yau Laraba ta ce jami’anta sun kama Lami Mai Rigima a Ƙaramar Hukumar Ardo Kola ranar Litinin da ta gabata.
Hukumar ta ce ta fara neman Lami tun daga Oktoban 2021, lokacin da aka kama da gurfanarwa da ɗaure wani mai suna Abdullahi Madaki mai shekara 50.
An kama sarauniyar da tabar wiwi da ta kai nauyin 150 giram, a cewar NDLEA.
Kazalika, hukumar ta kama wani mai suna Emeka Okiru mai shekara 40 da zargin mallakar ƙwayar tramadol 32,700 a Adamawan.
Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Burkina Faso Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai :
Wata kotun soja a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasa Blaise Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai sakamakon kama shi da hannu a kisan wanda ya gada Thomas Sankara.
An yi wa Compaore shari’a a bayan idonsa yayin da yake gudun hijira yanzu haka.
An yanke wa tsohon shugaban sashen tsaro na gwamnatinsa, Hyacinthe Kafando, hukuncin ɗaurin rai-da-rai shi ma.
Mista Sankara wanda ɗan neman sauyi ne mai aƙidar Markisanci, wasu ‘yan bindiga ne suka harbe shi a babban birnin ƙasar Ouagadougou a 1987.
Daga nan ne kuma Compaore ya mulki ƙasar tsawon shekara 27 har zuwa lokacin da aka tumɓuke shi a 2014.
Buhari ya kafa dokar kula da ofisoshin gwamnati a Najeriya :
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya wa wani Umarnin Shugaban Ƙasa 11 hannu da zai tabbatar da kula da ofisohsin gwamnati a faɗin ƙasar.
Buhari ya saka hannu kan dokar da ake yi wa laƙabi da Executive Order 11 jim kaɗan kafin fara zaman Majalisar Zartarwa a yau Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Jim kaɗan kafin saka hannun, Buhari ya nemi dukkan ma’aikatun gwamnati, da sashe-sashe, da hukumomi da su kafa sashen kula da tafiyarwa ƙarƙashin sabuwar dokar.
Bayan kammala sa hannun ne Buhari ya jagoranci zaman majalisar, wanda ministoci da sauran ƙusoshin gwamnati ke halarta.