Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 27.33 a watan Oktoba daga kashi 26.72 cikin 100 a watan Satumban 2023 ( NBS).
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta bayyana hakan a cikin rahotonta na kididdigar farashin kayayyaki da ta fitar a ranar Laraba.
Adadin na watan Oktoba ya nuna samun karin maki 0.61 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Satumban 2023.
Bugu da kari, a kowace shekara, farashi ya kan kai maki 6.24 cikin 100.
NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya kai kashi 29.29 cikin 100.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ya karu zuwa kashi 31.52 cikin dari, inda ya karu da maki 7.80 kuma shi ne mafi girma idan aka kwatanta da kashi 23.72 da aka samu a watan Oktoban 2022.
Alkaluman sun nuna cewa wannan shi ne karo na 10 da ake ci gaba da samun hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.
Wannan dai na zuwa bayan cire tallafin man fetur tare da wasu tsare-tsare da gwamnatin shugaba Tinubu ta kaddamar tun bayan kama mulki.
Hakan ya sanya a baya-bayan nan kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka yi yunkurin shiga yajin aiki.
A wani labarin na daban a daren Laraba ne majalisar zartaswa ta Kungiyar kwadago ta Nijeriya da kuma TUC suka yanke shawarar dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani da suke yi a fadin kasar.
Kungiyar ta ce, dakatarwar ta biyo bayan shiga tsakani da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya yi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, duka cibiyoyin kwadagon sun umurci mambobinsu da kungiyoyin da suke da alaka da su da su fara yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, 2023 kan cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero, da ‘yansanda suka yi a Owerri, jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba.
Cikakken labarai na zuwa daga baya…
Source: LEADERSHIPHAUSA