Mai Shari’a James Omotosho na kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ya haramta wa hukumar kula da kafafen sadarwa na gidajen Rediyo da talebijin (NBC) kakaba wa kafafen yada labarai biya tara ko takunkumi.
A hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, ta ce, NBC ba ta da karfin ikon yanke irin wannan tarar.
Mai Shari’a Omotosho, daga bisani ya dakatar da NBC daga lafta tara ga kafafen sadarwa a fadin kasar nan.
Kazalika, ya jingine tarar naira N500,000 ga kowace kafa har su 45 da aka ci tararsu a ranar 1 ga watan Maris din 2021.
Kotun ta ce, NBC ba kotun shari’a ba ce, don haka ba ta da karfin ikon da za ta sanya takunkumi ga kafafen sadarwa a matsayin ladaftarwa.
A cewar mai shari’an, dokar NBC da ya bai wa hukumar ikon kakaba takunkumin, ya ci karo balo-balo da sashi na 6 na kundun tsarin mulkin kasa da ya bai wa sashin shari’a wannan ikon.
Ya ce, kotun ba za ta zura ido haka nan tana kallon hukumar na sanya takunkumin ba bisa ka’ida ba.