Na’urorin Tashar Tattara wutar lantarki na TCN a Birnin Kebbi sun fashe a tsakiyar daren jiya Alhamis zuwa safiyar Juma’a.
Injinnan da ke samar da wutar lantarki a fadin Birnin Kebbi da kewaye sun fashe ba zato ba tsammani cikin dare, kafin fashewar an dawo da wutar lantarki.
Majalisa Ta Gayyaci Shugaban TCN Kan Badakalar Kudin Aikin Wutar Lantarki Dala Miliyan 33
Lantarki Ya Ɗauke A Faɗin Nijeriya, Yayin Da Tashar Samar Da Wuta Ta Ƙasa Ta Lalace
Birnin Kebbi na fama da matsalar lalacewar wutar lantarki daga cibiyar samar da wuta ta Kayinji na kasa.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:50 na daren ranar Alhamis zuwa safiyar Juma’a, an dawo da wutar da karfe 10 na dare. Amma wani yanki ya samu wutar lantarki da karfe 11 na dare.
Wani mazaunin kusa da tashar TCN, Malam Sule Shehu, ya bayyana cewa, da misalin karfe 10 na dare ne aka dawo da hasken wutar lantarki saboda mun shafe kwana daya ba tare da ganin kyallin hasken wuta ba sakamakon rugujewar wutar lantarki ta kasa, amma bayan kamar awa daya sai na ji wani abu ya fashe kamar bam, daga nan sai na ji karar fashewar wani abu na bugun wuta ko’ina.
“Kafin mintuna 10 mutane sun fito suna gudun kada fashewar ta raunata su suna ihu (wuta-wuta-wuta) a tashar tattara wutar lantarki ta TCN”. Cewar Sule Shehu
A kwanan baya an sanya sabbin injina a tashar tattara wutar lantarki ta TCN da ke cikin Birnin Kebbi, ana zaton sabbin injinan ne suka fashe sakamakon kura-kuran da ke tattare da su yayin da ake hada su.
Source: LEADERSHIPHAUSA