Mai Unguwar Nasara, Alhaji Nasiru Abdullahi Soja ya ce abin da ya faru da shi daga Allah ne baya zargin kowa, domin sai Allah Madaukakin Sarki ya yarda ne al’amura suke kasancewa.
- Nasiru Soja ya bayyana haka ne ranar Lahadi ta gabata lokacin da yake ganawa da manema labarai a dakin taro na Sahabi Hotel jim kadan bayan da aka kammala taron taya shi murnar samun ‘yancin kan shi, bayan wani ibtibla’i da ya same shi.
Wata kungiyar matasa na Maraba ce ta shirya masa wannan taron na taya shi murnar da dawowa daga gidan gyara halinka, inda aka tsare shi bisa zargin aikata laifi.
Ya ce zaman da ya yi a gidan gyara halinka ya koyi darussa da yawa na rayuwa, inda ya yanke shawarar zai ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi domin taimaka wa al’umma.
Bugu da kari, ya bayyana cewa bai rike kowa a zuciyansa ba dangane da abin da ya faru, wannan halin rayuwa ne, yana iya kasancewa yadda ba a taba tsammanin ba.
Ya yi ma bakin da suka halarci taron daga wasu wurare Allah ya sa su koma gida lafiya.
Da yake jawabi a madadin matasan da suka shirya taron, Abu Sufyan ya ce babban dalilin da ya sa suka shirya taron murnar dawowar Nasiru Soja shi ne, saboda nuna murna kan halinsa na kirki da yake yi wa al’umma.
Ya kara da cewa ba kowa ba ne zai iya yin haka, domin akwai masu halin da ya dace a ce suna yin hakan amma ba su yi.
Source: Leadership