Rahotanni sun tabatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe tsohon kwamishinan hukumar kula da yawan al’umma ta kasa wato NPC, Malam Zakari Umaru-Kigbu a jiahar nasarawa dake arewacin najeriya.
Bayanai sun ce lamarin ya auku ne da safiyar Lahadin nan a karamar hukumar Lafiya dake jihar Nasarawa, inda bayan kashe tsohon Kwamishinan, ‘yan bindigar suka yi garkuwa da ‘ya’yansa mata biyu.
Wani dan ‘uwan marigayin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar al’amarin ga jaridar Daily Trust a Najeriya.
Wasu majiyoyin kuma sun ce ‘yan ta’addan sun nemi a biya su naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kafin sako mata biyun da suka sace.
A wani labarin na daban rundunar sojin Jamhuriyar Congo da wasu kungiyoyin fararen hula sun ce, mayakan ‘yan tawaye sun kashe fararen hula da dama a wani kauye dake yankin Beni a gabashin kasar.
Sai dai wata kungiya dake sai ido kan batun tsaro da tashe-tashen hankula a gabashin Jamhuriyar ta Congo mai suna Kivu Security Tracker, ta ce akalla fararen hula 27 ne suka mutu.
An dai shafe tsawon lokaci ana zargin mayakan kungiyar ‘yan tawayen ADF da kashe dubban fararen hula a yankin gabashin jamhuriyar Dimokaradiyar Congo da ke fama da rikici.