Kungiyar daliban Nijeriya ta kasa NANS ta bayyana cewa, an kwaso daliban Nijeriya da suka makale a Khartoum babban birinin kasar Sudan, inda ake cigaba da gwabza yaki.
Jami’in yada labarai na kungiyar Amal Pantami ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar.
A cewar sanarwar, Manyan motoci kirar Bas 26 kowacce dauke da mutum kimanin 50 ne suka yi jigilar kwashe daliban daga babban birnin kasar, Khartoum.
Sanarwar ta nemi addu’o’in jama’a don fatan kowanne dalibi ya iso Nijeriya cikin koshin lafiya sannan kuma kungiyar ta yi godiya ga ‘yan Nijeriya bisa addu’oin da suke ci gaba da yi musu.
A ranar Lahadi gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta kashe dala miliyan 1.2 don kwashe daliban Nijeriya zuwa iyakokin kasar Masar, inda daga nan, za a kwashe daliban ta jirgin sama zuwa Nijeriya.
Rahotani sun ce, tun lokacin da aka fara yakin, a ranar 15 ga watan Afrilun 2023, sama da mutane 500 sun rasa rayukansu, inda kuma dubbai suka bar matsugunansu zuwa ketare.
Source:LeadershipHausa