Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta kasa (NANNM) reshan Jihar Kano, Kwamred Ibrahim Maikarfi Muhammad ya bayyana cewa hana likitoci fita wajen Nijeriya danyaen aiki ne, domin a nan gida Nijeriya ba a ba su hakkinsu yadda ya dace.
Kwamred Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tsokaci kan yunkurin hana likitocin Nijeriya fita kasashen ketare da cefanar da asibitoci a wata hira da manema labarai suka yi da shi a ranar Alhamis a ofishin kungiyar NANNM da ke Kano.
Ya ce wannan kungiya ta NANNM ba ta goyan bayan cefanar da asibitocin Nijeriya, domin jama’a ne za su kara shiga matsi, sannan ‘yan kasuwa su kara samun riba a bangaren harkar lafiya. Ya ce talakawa a halin yanzu sauki suke bukata ako ina cikin duniya, domin haka akwai bukatar hukumomi a kowane mataki su tashi tsaye wajen samar da kayan aiki da ma’aikata da inganta makarantu da cibiyoyin lafiya, musammam a Jihar Kano dama Nijeriya baki daya.
Haka kuma ya bayana kalubale uku da za a duba wajen warware matsalar korafe- korafe a asibutocin da ake samu yau da kullom, na farko akwai laifin hukuma na karacin ma’aikata da kayan aiki, sannan rashin samun cikakaken horo daga wasu ma’aikatan lafiyar ko rashin tarbiya na wasu ma’aikatan lafiyar ga kuma cinkoson aiki a asibutocin.
Ya ce akwai matsalar mutane na rashin wayewa ko hakuri wajen neman lafiya wanda suna bukatar kyakyawar fadakarwa daga hukuma na sanin hakin ma’aikacin lafiya da kuma hakinsu na masu neman lafiya ta yadda kowa zai kiyaye doka da ta hau kansa da dai sauransu.