Najeriya zata tarwatse muddin ‘yan Arewa suka ci gaba da mulki a 2023 _Ohanaeze Indigbo.
Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta yi gargadin cewa, Najeriya zata tarwatse muddin ‘yan Arewa suka ci gaba da mulki a shekarar 2023.
Kungiyar ta gargadi ‘yan siyasar Arewa wanda tace idanunsu sun kulle da neman shugabancin Najeriya da su daina nema ci gaba da mulki a 2023.=
Kungiyar tace akwai alkawari da aka yi tsakanin ‘yan kudu da ‘yan Arewa wanda na karba-karbar mulki wanda kuma idan ba ci gaba da wannan alkawarin ba akwai matsala.
Tace domin zaman Lafiya ya kamata a baiwa kudu mulkin Najeriya.