Najeriya; Zaben Fitar Gwani Na ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC A Zaben 2023.
A ranar yau Litinin shida ga watan Yuni ne jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, take fara gudanar da zaben fitar da gwani na masu son yi mata takarar shugabancin kasar a zaben 2023.
Jam’iyyar ta APC ta kayar da jam’iyyar PDP a zaben 2015 bayan, PDPn ta kwashe shekara goma sha shida tana mulki. Manyan ‘yan jam’iyyar ne suke fafatawa domin ganin sun maye gurbin shugaban kasar Muhammadu Buhari a zaɓen 2023.
Kowanne ɗan takara ya bayyana manufofinsa da yake fatan ganin ya cimma idan ya yi nasara.
Cikinsu akwai mataimakin shugaban kasa da tsoffin gwamnoni da tsoffin ministoci da kuma ‘yan majalisar dattawa.
Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo na daya daga cikin na farko-farko da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Farfesa Osinbajo ya bayyana tsayawa takarar ce a wani jawabi ta bidiyo da aka yada ta talabiji da sauran kafofin sada zumunta inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.
Osinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari’a na Jihar Legas ya zama mataimakin shugaban ƙasa, ya ce ya tsaya takara ne domin inganta rayuwar ‘yan kasar yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa yana da kwarewar shugabancin Najeriya.
“A cikin shekara bakwai, na bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban kasa, na wakilci kasar nan a muhimman ɓangarori a ƙasashen waje. Na ziyarci kusan kafatanin kananan hukumomin Najeriya. Na je kasuwanni, da masana’antu, da makarantu da gonaki,” in ji Farfesa Osinbajo.