Najeriya za ta sake ɗauko likitocin ƙasar da ke aiki a ƙasashen waje
Ministan Lafiya na Najeriya dakta Osagie Ehanire, ya ce gwamnatin tarayya na wani shiri domin maido da likitoci da ma’aikatan jinya ‘yan asalin ƙasar da ke aiki a ƙasashen waje, tare da maida su aiki a jami’o’i da asibitocin ƙasar.
Yayin da yake jawabi a wajen gabatar da nasarorin da ma’aikatun gwamnatin tarayya suka samu ƙarƙashin wannan gwamnati ranar Talata a Abuja babban birnin ƙasar, ministan ya ce ya fahimci yadda ƙwararrun likitoci ke bariin ƙasar.
Ministan ya ce da yawa daga cikin likitoci da ma’aikatan jinya suna ganin kamar ba a biyansu ladan aikin da suke yi kamar yadda ya kamata.
Mista Ehanire ya ce gwamnatin tarayya na ƙoƙarin magance matsalar ta hanyar inganta yanayin aikin likitocin.
Ya ƙara da cewa matsalar ƙarancin likitoci matsala ce da ta shafi duniya baki-ɗaya, ba Najeriya kaɗai ba.
Ya ci gaba da cewa ”A wani zama da muka yi da ministan lafiya na ƙasar Gambiya ya yi min ƙorafi game da yadda likitoci ke barin ƙasar”.
”Sannan kuma na zanta da hukumomin Birtaniya waɗanda suma suka sanar da ni cewa mafi yawan likitocin ƙasar na tafiya Canada da New Zealand inda ake biyan albashi mai gwaɓi, dan haka suke buƙatar ƙarain likitoci a ƙasarsu, sannan haka lamarin yake a Masar da Turkiyya”.