Najeriya ; ‘Yan Bindiga 80 Daga 25 Ga Watan Maris Zuwa 7 Ga Afirilu.
Hedikwatar Hukumar tsaron kasa DHQ ta bayyana cewa dakarun Najeriya dake aiki a karkashin rundunonin Operation Thunder Strike, Safe Haven, Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga 80 a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka a Abuja da yake bada bayanai game da aiyukan da dakarun suka yi daga ranar 25 ga Maris zuwa 7 ga Afrilu.
Onyeuko ya ce a jihohin Kaduna da Niger Operation Thunder Strike sun kashe ‘yan bindiga 34 sannan sun kama bindigogi 14 da babura 17.
Ya ce a ranar 30 ga Maris rundunar sojin sama ta kashe ‘yan bindiga da dama a kan babura dake wucewa ta hanyar Akilibu-Sarkin Pawa a kauyen Mangoro dake tsakanin jihar Kaduna da Niger.
Rundunar ta kuma kashe ‘yan bindiga 33 ranar 30 ga Maris bayan rundunar sojin sama ta hango ‘yan bindigan a jirgi a kusa da Kusasu.
Ya ce rundunar Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga 10, sun ceto mutum 5 da aka yi garkuwa da su sannan sun kama ‘yan bindiga 7 a jihohin Sokoto da Zamfara.
Rundunar ta kuma kwato makamai da dama a tsakanin wannan lokaci.
Onyeuko ya ce Operation Whirl Stroke ta yi sintiri a bangarori da dama domin ganin ta rage ayyukkan ‘yan bindiga.
Rundunar ta kama ‘yan bindiga 9, ta kashe 3 sannan ta kama mamamai da dama.