’Yan majalisa masu waklitar Najeriya a kungiyar ECOWAS sun yi barazanar ficewa daga kungiyar saboda saba wasu ka’idojojin daukar aiki wanda haka bai yi wa Nijeriya dadi ba.
- Wasu ‘yan majalisar dokokin kungiyar da suke wakiltar Najeriya ne suka yi wa manema labarai bayani, sun bayyana cewa, a zaman majalisar na 2022 da aka yi a Abuja ranar 3 ga watan Yuli suka jagoranci yanke hukuncin zartas da dakatar daukkan shirin daukar ma’aikata a kungiyar
Matsalar Tsaro: An Kashe Mutane 14,500 A Yammacin Afirka Cikin Shekaru 4 – ECOWAS
Sun kara da cewa, shawarar ta biyo bayan rahotannin da aka samu na rashin bin ka’aida da rashin adalci da ke tattare da shirin daukar ma’aikatan, inda aka yanke hukuncin dakatar da shirin har sai an samu cikakken rahoto daga kwamitin binciken da aka kafa.
Yan majalisar daga Najeriya sun kuma yi nuni da irin dumbin gudummawar kudade da Nijeriya ke bayarwa ga kungiyar duk kuwa da matsalolin da kasar ke fuskanta.
A wani labarin na daban a ranar Juma’a majalisar masarautar Bichi ta gudanar da addu’o’i na musamman don neman taimakon Allah a kan matsalar tsaro da ake fuskanta a sassan kasarnan.
Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, ya jagoranci zaman addu’o’in a babban masallacin Juma’a na Bichi.
Manyan Malamai da Limamai daga kananan hukumomi 9 na masarautar a karkashin jagorancin babban limamin Bichi, Malam Khalifa Lawan Abubakar, ne suka gabatar da addu’o’in.