Najeriya; Ta Yi Alkwarin Sakin Kudaden Kamfanonin Jiragen Sama Na Kasashen Wajen Da Suka Makale.
Ministan watsa labarai a tarayyar Najeriya ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba za’a sakewa kamfanonin jiragen sama na kasashen waje wadanda suke aiki a kasar kudaden kimani dalar Amurka Miliyon $464 da suka makale.
Jaridar leadership ta Naigeriya ta nakalto, Alhaji Lai Muhammed, yana fadar haka a bikin bude sabon “ taminal na biyu” a tashar jiragen sama ta Murtala Muhammad dake Lagos. Tuni dai kamfanin zirga –zirgan jiragen sama na ‘Emirates Airlines” ya bada sanarwan dakatar da zuwa Najeriya daha ranar 1-Satumban -2022 saboda makalewar kudaden kamfani a Najeriya.
A wani bangaren kuma hukuma mai kula da tashoshin jiragen sama FAAN ta bada sanarwan cewa ba zata kara farashin sauka da tashi da kuma ajiye jiragen sama na ci da na kasashen waje a dukkan tashoshin jiragen sama na kasar b.
Shugaban hukumar FAAN, Captin. Rabiu Yadudu, ya fadawa yan jarida kan cewa sabbin kamfanonin jiragen sama 5 ne zasu fara samfani da sabon taminal 2 wanda aka kammala a tashar jiragen sama na Lagos. Sannan ya kara da cewa Taminal 2 zata samar da ayyuka kimani 10,000 ga yan kasa kai tsaye ko da wasida. Sannan yana da damar karban fasinjoji har miliyon 14 a ko wace shekara.