Tsohon kocin tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya, Isma’ila Mabo ya bayyana cewa, Hukumar Kwallon Kafar kasar NFF ba ta yi masa wani tanadi ba domin halartar gagarumin bikin karrama tsoffin ‘yan matan na Super Falcons da aka gudanar a birnin Lagos a farkon wannan makon.
Kazalika ya jagoranci wannan tawaga har zuwa matakin wasan dab da na kusan karshe a Gasar Motsa Jiki ta Olympics a 2004.
Rashin halartar kocin wannan gagarumin biki a Lagos a ranar Litinin da ta gabata, ya haifar da kace-nace a Najeriya, inda wasu ke ganin cewa, har yanzu ana fama da matsalar nan ta an ci moriyar ganga, an yada kwaurenta.
Koda yake Mabo ya ce, NFF ta yi kokarin tuntubar sa amma ta hanyar wata mamba a kwamitin da ya shirya bikin karramawar, amma duk da haka babu wani tanadi da aka yi masa a cewarsa.
Kawai dai an sanar da shi cewa, za a gudanar da bikin ne kadai, amma babu wani karin bayani inji shi.
Daga cikin ‘yan matan da aka gayyato domin karrama su har da wadanda ke zaune a Amurka da wasu kasashen Turai, yayin da matan suka bayyana takaicinsu na rashin tozali da tsohon kocin nasu a wurin bikin.
A wani labarin na daban hukumar UEFA ta sanar da linka kudin kyautar da za ta bai wa tawagogi 16 da za su taka leda a gasar cin kofin EURO 2022 ta mata.
Sanarwar da UEFA ta fitar game da karin kudaden da masu halartar gasar za su samu, ta ce kasashe 16 za su raba kudin da yawansa ya kai yuro miliyan 16 sabanin yuro miliya 8 da suka karba a shekarar 2017.
Matakin a cewar UEFA kokari ne na kara yawan kudin da ake kashewa gasar ta mata don gogayya da makamanciyarta ta Maza da ta gabata cikin watan Yuni zuwa Yuli.
Haka zalika UEFA ta kuma sanar da ware yuro miliyan 4 da rabi ga kungiyoyin Turai da suka amince da sakin ‘yan wasansu don halartar gasar.
Akalla tikitin kallon wasan dubu 700 za a sayar a wannan karo duk dai a kokarin kawata gasar ta mata mafi girma a Turai.