Gwamnatin Najeriya ta sanar da gano wani sabon arzikin iskar gas da yawan sa ya kai triliyan 206 a ma’aunin cubic lokacin da take aikin neman man fetur.
Karamin ministan man fetur din kasar Timipire Sylva yace kasar na iya gano wani karin iskar gas din da zai kai triliyan 600 wanda za tayi amfani da shi wajen bunkasa harkar ci gaban ta.
Sylva yace sun tsinci dami a kala ne wajen gano arzikin iskar gas din lokacin da suke fafutukar neman karin man fetur, abinda zai taimakawa kasar wajen rage dogaro da man fetur wajen komawa amfani da iskar ta hanyar girki da motoci da kuma masana’antu.
Sylva yayi watsi da masu sukar kasar akan ci gaba da dogaro da wannan arzikin a daidai lokacin da kasashen duniya ke amfani da sabbin dabarun dake samar da makamashin da basa gurbata muhalli, inda yake cewa sannu a hankali idan kasar ta bunkasa wadannan hanyoyi zata kaiga zuwa matakan da suma manyan kasashen suka samu kan su.
Ministan yace ya zuwa wannan lokaci makamashin da ake amfani da shi a Najeriya da kuma kasashen Afirka bai kai kashi guda daga cikin hayakin da sauran kasashen duniya ke fitarwa suna gurbata muhalli da shi ba.
Najeriya na cikin matsalolin tsaro wanda ake ganin ya samo asali ne daga tsomala bakin kasashen yamma wadanda aske zargi da shigowa domin debo dukiyar da ke dankare a najeriya amma kuma suke amfani da yada rashin tsaro da ta’addanci domin tabbatar da bukatun su na deban dukiya.
Masu lura da lamurran siyasar najeriya suna ganin wannan lamari abin tsoro ne domin zai kara janyo hankalin wadancan kasashen na yammacin turai kan najeriyar sakamakon sabbin ma’adanai da ake samu a kasar.
Tare dai da yawaitar arziki a najeriyar amma kullum mizanin talauci yana karuwa tsakanin mutane sakamakon ba’a amfani da dukiyar domin samar da jin dadin al’umma.