Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi nasarar gano tare da tsare wasu fitattun mutane da ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a kasar kamar yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana.
Mun toshe kafofi masu nasaba da samar da kudaden, sannan mun fara gudanar da gagarumin bincike wanda ke haifar da da mai ido a kokarin yaki da ta’addanci. inji Malami
Koda yake Malami ya ce, ba zai yi rika malam masallaci ba wajen zurfafawa a cikin bayanansa saboda a haklin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
A cikin watan Mayun da ya gabata ne Malami ya ce, gwamnatin Najeriya na shirin fara tuhumar wasu mutane 400 cikinsu kuwa har da wasu fitattu da ake zargi da bai wa Boko Haram kudaden tallafi.
Sai dai an yi ta caccakar gwamnatin kan jinkirta tuhumar mutanen, amma Malami ya bada tabbacin cewa, gwamnatin tarayyar ta dukufa wajen daukar tsauraren matakan yaki da ta’addanci a kasar, yana mai bada da misali da irin nasarar da ake samu kan mayakan Boko Haram da kuma ‘yan bindiga da suka addabi kasar.
A wani labari na daban rundunar Sojin Najeriya ta yi ikirarin cewa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen hana kungiyar ISWAP aiwatar da kudirinnta na rusa kasar, bayan da ta ke ci gaba da karfafa hare-harenta musamman yankin arewa maso gabas.
A cewar Janar Musa yayin wata zantawarsa da manema labarai a birnin Maiduguri na jihar Borno, zai fi dacewa ga wadanda ke marawa kungiyar baya kama daga mayaka da kuma daidaikun jama’a, su sani cewa ISWAP ba ta da hadi ta kowacce fuska da Najeriya, kuma manufarta shi ne ruguza kasar.
Acewarsa ISWAP kungiya ce da wasu ke daukar nauyinta daga ketare don kaddamar da hare-hare a sassan Najeriya ta yadda za ta samu gurbin mamaya a kasar.
Ko a makon da ya gabata sai da kungiyar ta ISWAP ta kashe sojin Najeriya 18 baya ga jikkata wasu 11 baya ga yin garuwa da wasu Sojin 2, harin da yak e matsayin mafi muni da kungiyar ta kaddamar tun bayan rahoton kisan jagoranta.