Najeriya; Shugaban Buhari Ya Bayyana Cewa An Kusan Kawo Karshen ‘Yan Ta’adda A Kasar.
A sakonsa na salla karama shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai fatan za’a kawo karshen ayyukan yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a kasar nan gaba kadan.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Najeriya NAN ya nakalto mai bawa shugaban kasar shawara kan al-amuran watsa labarai Malam Shehu Garba yana fadar haka a matsayin goron salla daga shugaba Buhari ga musulmi wadanda suke bukukuwan salla a yau Litinin.
A cikin wani rahoto a robice da ya karanta a madadin shugaban. Shehu Garba nakalto shugaban yana cewa a watan da ya gabata an kashe shugaban kungiyar ISWAP sannan dubban mayakan kungiyoyin Boko Haram da na Iswab suna mika kansu da makamansu ga sojojin kasar.
READ MORE : Siriya; An Yi Kokarin Kishe Shugaban Asad Ba Tare Da Samun Nasara ba.
Dangane da karuwar satar danyen man fetur a kudancin kasar kuma shugaban ya ce duk tare da labarai masu dadi da suke fitowa daga yankin na kokarin tsabtace yankin daga gurbatavccen man fitur, amma har yanzun wasu marasa kishin kasa suna kara gurbata yankunan da ake hakar mai a cikinsu.
READ MORE : Najeriya; Lawal Ya Bukaci A Sasanta Da ASSU A Ranar Ma’aikata.