Najeriya; Shugaba Buhari Yayi Allawadai Da Kissan Wata Daliba Kirista A Sokoto.
Shugaban Muhammadu Buhari ya yi allawadai da kissan da wasu jama’a suka yiwa wata daliba, wanda take shekara ta biyu a kolajin Shehu Shagari ta tarbiyyan malamai dake sokoto a ranar Alhamis.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban yana fadar haka ta bakin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai Malaman Garba Shehu.
Shugaban ya ce bai kamata mutane su dauki doka a hannunsa ba ko da kuwa hakan ya faru. Haka ma mataimakin shugaban kasa Proff. Yeme Osingbajo ya nuna takaicinsa dangne da kissan Deborah Samuel kan zargin batanci da manzon All..(s). Osingbaji ya kara da cewa, akwai abin takaita da yadda mutane suke daukar doka a hannunsu, bayan ga akwai hukumomin da yakata su kula da irin wannan lamarin.
READ MORE : Daga Khashoggi zuwa Shereen Abu Akleh, Kisan ‘Yan Jarida ta Gwamnatin Danniya.
Daga karshe ya bukaci a gaggauta zakulo wadanda suka yi hakan sannan a hukunta su. Sannan ya mikla ta’ziyya ga iyalan Deborah Samuel wacce aka kashe a sokoto.
READ MORE : Martanin wasu kasashen Africa game da kisan da Isra’ila ta yi wa dan jaridar Al-Jazeera.
READ MORE : Nasrallah; Wadanda Suke Neman Sasantawa Da Isra’ila Sun Kunyata Tare Da Kissan Abu-Akleh.