Hukumomin Najeriya sun ce sun fara tattaunawa da kamfanin Twitter na Amurka domin warware matsalar da aka samu a tsakanin su bayan dakatar da shi daga aiki a kasar.
Dakatar da kamfanin ya haifar da muhawar mai zafi tsakanin masu goyan bayan matakin da masu adawa da shi.
Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama ya tabbatar da tattaunawar bayan ganawa da Jakadun wasu kasashe kan dalilin daukar matakin.
A makon jiya Amurka ta soki lamirin gwamnatin Najeriya a game da dakatar da dandalin sada zumunta na Twitter a kasar, tana mai bayyana matakin a matsayin sako mara armashi ga al’umar kasar da ma masu zauba jari a cikinta.
A martanin da ta mayar a wata sanarwa, fadar gwamnatin Najeriya ta kare haramcin da ta yi wa Twitter, tana mai cewa dandalin Twitter ya dade yana tabargaza a kasar kuma ba a daukar mataki.
A wani labarin na daban kamfanonin sadarwa a Najeriya da suka hada da MTN da Airtel da Glo da kuma 9Mobile sun fara toshe hanyar shiga shafin, Twitter a yau, kwana daya bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da shafin a Najeriya.
Kamfanonin sun ce sun samu umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya don toshe hanyoyin shiga shafin Twitter a kasar bayan dakatarwar na Gwamnatin Tarayya a ranar Juma’a.
‘Yan Najeriyar masu amafani da shafin sun farka a ranar Asabar da fuskantar wahala wajen samun damar shiga shafukansu na Twitter yayin da wasu ke lalubo wasu hanyoyin sadarwar masu zaman kansu.
Fittatu sunyi tir da matakin
Tuni fitattun ‘Yan Najeriya da shahararrun suka fara nuna bacin ransu danagane da matakin na Gwamnatin Tarayya na hana amfani da Twitter a kasar, ba tare da la’akari da kutse da shisshigin da Twitter ke wa gwamnati ba.
Aisha Buhari ta rufe Twitter
Tuni mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari ta rufe shafinta na Twitter, domin biyayye da umurnin da uban ‘ya’yan nata yayi.
“Zan rufe shafina na Twitter a yanzu. Fatan alheri ga Najeriya,” kamar yadda ta rubuta gabanin rufe shafin.
PDP
Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta bi sahun wasu fitattu da suka hada mawaka da lauyoyi wajen Allah wadai da matakin gwamnatin tarayya na katse Twitter.