Buhari ya ce za a karbo rancen ne daga Bankin Duniya da Hukumar tallafawa ci gaban kasashe ta Faransa da kuma Bankin EXIM da ke Amurka da kuma Asusun Tallafawa Noma na Duniya IFAD.
Shugaban Najeriyar ya ce rancen zai bai wa Gwamnatinsa damar aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa a sassa daban-daban.
A wani labarin na daban kungiyar Kwadago a Najeriya ta gargadi gwamnatin kasar da kada ta kuskura tace zata zabtare albashin ma’aikatan ta sakamakon matsalar kudaden da tace tana fama da shi.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba yace bai dace ace gwamnati ta rage mafi karancina labashin da ake biya ba na naira 30,000 wanda a halin yanzu ko buhun shinkafa ba zai iya saye ba.
Waba yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ja kunnen ministan wajen ganin ta janye kalaman ta da kuma dakatar da duk wani yunkuri na rage albashin.
Wannan ya biyo bayan sanarwar da minister kudi Zainab Ahmed tayi cewar gwamnatin na nazarin rage tsadar kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da ayyukan ta wanda ya hada da rage albashin ma’aikata.
Ministar tace tuni ta baiwa Hukumar dake kula da albashin ma’aikata umurnin sake Nazari kan albashin ma’aiaktan gwamnatin tarayya da kuma yawan hukumomin da ake da su domin bada shawara akai.
A yanayin matsin rayuwa da tattalin arziki da ake ciki zai zama rashin imani mafi girma a sake bullo da wasu hanyoyi da kuntata ma mutane musamman maganar taba albashin ma’aikata wacce ta shafi talakawan kasa kai tsaye.