Kawo yanzu dai, rundunar sojin saman Najeriya ba ta tabbatar ko musanta adadin wadanda aka kashe ba, saidai mai Magana da yawunta Edward gabkwet, ya fitar da sanarwar da ke cewa, tabbas sun samu rahoto kan lamarin kuma sun kaddamar da bincike kan zargin.
Mazauna kauyen na Buhari da dama sun ce jirage masu saukar ungulu uku sun yi ta shawagi a yankin nasu, daga bisani kuma daya daga cikinsu ya bude wuta.
Wani mazaunin kauyen Grema Zanna ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ya shaida binne mutane 10, yayin da kuma aka garzaya da wasu 22 zuwa asibiti.
Najeriya ta shafe shekaru 12 tana fama da rikicin Boko Haram da yafi shafar yankin arewa maso gabashin kasar, wanda ya yi sanadin kashe mutane sama da dubu 40 tare da raba wasu mutanen kusan miliyan 2 da gidajensu.
Bayanai sun ce tawagar dakarun Najeriya sun gamu da turjiyar ce yayin da suke kan hanyar zuwa sansaninsu dake Buni Yadi.
Sai dai cikin sanarwar da fitar ranar Lahadi a hukumance, rundunar sojin Najeriya tace sojanta 1 ne kawai ya mutu yayin fafatawar da suka yi da ‘yan ta’addan a ranar Asabar, kuma sun samu nasarar kashe 28 daga cikinsu.
A shekarar 2016 kungiyar Boko Haram ta rabu zuwa gida biyu, abinda ya bada damar kafuwar mayakan ISWAP da suka yiwa kungiyar IS mubaya’a.