Najeriya; Ministoci 10 Ne Suka Ajiye Ayyukansu Don Shiga Takarar Zaben Shekara Mai Zuwa.
Ministoci 10 suka ajiye ayyukansu saboda shiga takarar neman kujeru daban-daban na shugabanci a zaben shekara mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan watsa labarai Mr Lai Muhammad yana fadar haka a jiya Jumma’a . Ya kuma kara da cewa ajiye ayyukan ya zo ne bayan da shugaban kasa ya bada sanarwan cewa duk wanda yake son shiga harkokin siyasa a kasar daga cikin ministocinsa to su yi hakan kafin 16 ga watan Mayun da muke ciki.
Ministocin da suka ajiye ayyukansu dai sun hada da na karamin minister a ma’aikatar man fetur, Ministan sharia, Sifili, kwadago,Niger Delta, kimiyah da Fasaha da kuma na Mata.
Banda haka karamin miministoci na ma’adinai da ilmi duk sun ajiye ayyukansu. Dokan dai ta kebe mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya shiga takarar neman shugabancin kasar a jam’iyarsa ta APC.
A karshen wannan watan ne ake saran jam’iyyar APC mai mulki zata yi zaben fidda yan takara a mukamai daban-daban daga ciki har da na shugaban kasa a zaben na shekara ta 2023. ‘Yan takari kimani 20 ne suke neman tsayawa jam’iyyar ta APC takarar shugaban kasa.