Najeriya; Masu Zanga-Zanga Sun Fito Don Nuna Goyon Bayan Kungiyar Malaman Jami’o’I ASSU.
Tun ranar talata da kuma jiya Laraba ce kungiyar gwadago ta Najeriya NLC ta bukaci yan Najeriya a duk fadin kasar su fito zanga zangar neman gwamnatin tarayyar ta sasanta ko ta biya bukatun kungiyar malaman Jami’o’ii a kasar wato ASSU wadanda suke yajin aiki kimani watanni 6 a halin yanzu.
Jaridar Leadership ta Najeriya ta bayyana cewa a jiya Laraba an gudanar da zanga-zangar goyon bayan ASSU a birnin Abuja babban birnin kasar . Wani shugaban kungiyar Kwadago na kasar ya rubuta a kan cewa muna zanga zangar neman yarammu su koma karatu.
READ MORE : Tattaunawar Makamin Nukilya: Iran Tana Maraba Da Hanyoyin Diflomasiyy.
Kungiyar ASSu dai tana bukatar gwamnatin tarayyar Kasar ta cika alkawulan da ta cimma da kungiyar a shekara 2009 da ita. Har’ila yau da kuma canza tsarin biyan albashi na IPPIS da tsarin biya na da wato UTAS. Tun ranar 14 ga watan Fabrairu ne malaman suka fara yajin aiki, sannan suka yi ta jan lokacin har ya zama sai illamashaallahu.
READ MORE : Iran Da Gaske Take Tana Bukatar Yarjeniya Mai Karfi Dangane Da Dage Mata Takunkuman Tattalin Arziki.
READ MORE : Shugaban Kasar Faransa Ya Ce Rasha Tana Amfani Da Abinci A Matsayin Makami.