Najeriya; Malaman Jami’o’i Sun Tsawaita Yajin Aikin Da Suke Ciki Da Makonni 8.
Majiyar kungiyar malaman jami’o’ii a Najerita ta bayyana cewa kungiyar malaman ta tsaidawa shawarar tsawaita yajin aikin da suka shiga zuwa wasu makonni 8, ko kuma zuwa lokacinda gwamnatin tarayyar kasar ta ga yakamata ta waiwayesu.
Jaridar Premium times ta Najeriya na kalato wani wanda baya son a bayyana sunansa cikin kwamitin gudanarwa na kungiyar ta ASSU yana fadar haka a safiyar yau Litinin bayan da suka kammala taron da suka fara jiya lahadi da yamma.
An gudanar da taron majalisar zartarwa da kungiyar ASSU ne a babban cibiyanta dake birnin Abuja babban birnin kasar.
READ MORE : Yahudawan Iran Na Goyon Bayan Hare-Haren Da Aka Kai Kan Cibiyar Sahyoniya A Arbil.
Wata guda kenan da fara yajin aikin da malaman jami’o’in gwamnati a Najeriya suka fara yakin aiki tare da bukatar gwamnatin tarayyar kasar ta cika alkawulanda ta amince zata yi masu, a shekarun da suka gabata.
Kungiyar tana samun sabawa da gwamnatin tarayyar a cikin al-amura da dama, saga ciki akwai tsarin biyan albashi, da kyautata yanayin jami’o’in gwamnatin kasar ta bangaren kayakin karatu da kuma kala da jami’o’in kamar yadda yakamata.
READ MORE : Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Takwaransa Na Ukraine.