Najeriya; Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kafa Rundunar Tabbatar Da Tsaro Ta Mafarauta.
Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta amince da kudurorin kafa sabbin rundunonin jami’an tabbatar da zaman lafiya na ‘Nigerian Peace Corps’ da kuma rundunar mafarauta ‘Nigerian Hunters Council Bill’ domin taimakawa jami’an tsaro wajen dakile kalubalen tsaro da ya addabi kasar.
Kudirin dokar kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya ta 2020 ya samu amincewar Majalisar ne bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar kan harkokin cikin gida.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu ne ya gabatar da daftarin kudirin, sakamakon matsalolin tsaro da suka ki suka ki cinyewa a Najeriya.
A lokacin da yake gabatar da rahoton kwamitin a madadin Shugaban kwamitin Sanata Kashim Shettima, Sanata Suleiman Sadiq Umar ya ce kwamitin nasu ya hade Kudirin ‘Nigerian Peace Corps’ da ta National Unity Corps zuwa wuri guda don saukaka aiki, bisa la’akari da cewa duk kusan tsari daya ne suke kunshe da su.
Ya ce kudirin rundunar tabbatar da zaman lafiyar zai baiwa matasa da dama guraben aikin yi, baiwa masu son bada gundumawar kyautata zaman lafiya dama, da kuma hidimta ga jama’a, gami da gina ci gaban kasa.
Sadiq ya ce rundunar za ta dauki nauyin horar da matasa kan hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, kiyaye tashin-tashina, bada ilimi kan zaman lafiya, kwantar da hankula a yayin tarzoma da daidaita lamura a tsakanin al’ummomin kasa.
Sanata Sadiq Umar ya ce rundunar Mafarauta ‘Nigerian Hunters Council Bill’ za ta bada dama wajen inganta lamuran tsaro musamman wajen dakike aniyar ‘yan ta’addan da suke buya a cikin dazuka.