Najeriya; Litinin 13 Ga Watan Yuni Hutu Ce Don Raya Ranar Demokradiyya A Kasar.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta maida ranar litinin mai zuwa wato 13 ga watan Yuni a matsayin ranar raya democradiyya a duk fadin kasar.
Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto ministan al-amuran cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola yana fadar haka a madadin gwamnatin tarayyar kasar, ya kuma taya mutanen kasar murnar zagayowar wannan ranar, ya kuma bukaci ‘yan kasar da su rungumi zaman ljuna don tabbatar da zaman lafiya hadin kai da kuma aiki tare.
Ministan ya kara da cewa duk tare da matsalolin da kasar take fuskanta, amma gwamnatin mai ci tana iya kokarinta don samar da kasa guda wacce hada dukkan mutanen kasar don samun ci gaba da hadin kai mai doraewa.
READ MORE : Ra’isi; Ba Wata Kasa A Duniya Wacce Zata Tursasawa Iran Yi Ko Barin Wani Abu.
A wani bangaren na jawabinsa Ogbeni Rauf Aregbesola ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta yi abinda yakamata ta yin a girmama MKO Aboila wanda ya lashe zaben shekara 1993 a ranar 12 ga watan Yunin wancan shekara, amma aka bata sakamakon zaben.
READ MORE : A Jiya Jumma Ce A Ka Yi Bukukuwan Haihuwar Limani na 8 Daga Limamai Masu Tsarki.