Najeriya Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASSU) Zata Dakatarada Karantarwa Na Gwana Guda.
Majiyar kungiyar malaman jami’o’i a tarayyar Najeriya (ASSU) ta bada sanarwan cewa zata dakatar da karatu na kwana gudu, wato gobe litinin a duk fadin kasar a matsayin gargadi ga gwamnatin tarayyar kasar, kan rashin cika alkawalin da ta yi da kungiyar a shekara ta 2020.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ASSU tana cewa dakatar da karatu a gobe Litinin 7 ga watan Fabrairu gargadi ne ga gwamnatin tarayyar kasar, kan matakin da zata dauka a nan gaba.
Har’ila ASSU ta ce dakatar da karatun zai zama farkawa ga sauran ma’aikatan Jami’o’in kasar kan irin halin da malaman su ke ciki. Sannan sauran mutanen kasar ma su san cewa idan malaman sun shiga yajin aiki na gaba, to gwamnatin tarayyar ce ta jawo hakan. Saboda ta kasa cika alkawarin da ta dauka a shekara ta 2020, wanda ya kawo karshen yajin aiki na watanni 9 da malaman jami’an suka yi kafin su koma bakin aiki.