Najeriya; Kungiyar Kamfanonin Jiragen Sama Za Ta Dakatar Da Zirga-Zirgar Jirage A Cikin Gida.
Kungiyar Masu kamfanonin jiragen sama ta Nijeriya (AON) ta sanar da dakatar da ayyukanta daga ranar litinin mai zuwa, sakamakon tashin gwauron zabi da farashin man jirgin saman (Jet A1) ya yi, wanda ya kai Naira 700 akan kowacce lita.
Hukuncin dakatar da sufurin na kunshe ne Cikin wata takarda da shugaban kungiyar Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya aikewa ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika.
“Farashin man jirgin (JetA1) ya tashi daga Naira 190 kan kowace lita zuwa Naira 700 a halin yanzu, inda kungiyar ta ce babu wata kasa a duniya da irin haka ta taba faruwa a lokaci guda.
Bayanin kungiyar ya kara da cewa, a harkar sufuri ta duniya kudin man jirgin shi ke lakume kashi 40 cikin dari na kudin da kamfanonin ke samu a harkar jiragen, a yanzun karin da aka yi na kudin man jirgin, ya ninka har sau Kashi 95.
Kamfanonin jiragen saman suna neman Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta kasa da Kamfanin NNPC da ’yan kasuwa a bangaren hada-hadar mai, da su duba lamarin su rage farashin man jirgin (JetA1).
Yanzu haka dai farashin kujera matsakaiciya a tafiyar tsawon sa’a guda zai Kai Naira N120,000, abin da bai taba faruwa ba a tarihin Najeriya.