Najeriya; Jam’iyyar PDP Ta Lallasa APC A Zaben Gwamnan Jihar Osun.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ayyana Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Osun.
A ranar Asabar ne aka gudanar da zaben gwamnan cike da tsauraran matakan tsaro.
Babban baturen zaben Jihar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ya ce Sanata Adeleke ya samu kuri’a 403,371
Gwamna mai-ci Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’a 375,027.
Bayanan da INEC ta fitar na kananan hukumomi 30 da ke jihar sun nuna cewa PDP ta yi nasara a kananan hukumomi 17 yayin da APC ta samu kananan hukumomi 13.
Dama dai a baya Gwamna Oyetola, wanda ya so yin ta-zarce karo na biyu, ya kayar da Sanata Adeleke.
Rahotanni sun ruwaito cewa tun cikin dare ranar Lahadi zuwa wayewar gari aka fara karbar sakamakon zabukan da aka yi daga matakin kananan hukumomin jihar.
Zababben gwamnan, mai shekara 62, dan asalin karamar hukumar Ede ne.
Ya wakilci yankin Osun ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party daga 2017 zuwa 2019.
Ya tsaya takarar Sanata ne bayan rasuwar dan uwansa Sanata Isiaka Adeleke.
A shekarar 2018 ya tsaya takarar gwamnan Jihar Osun amma ya sha kaye a hannun Mista Oyetola.
Ya kammala Digirinsa na farko ne a fannin nazarin aikata laifuka a Kwalejin Atlanta Metropolitan State College da ke Amurka.