Najeriya; Jam’iyyar APC Ta Zabi Sanata Abdullahi Adamu A Matsayin Sabon Shugabanta.
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zabi Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugabanta.
A cikin wata sanarwa kan hakan a yayin babban taron jam’iyyar, Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru ya bayyana cewa dukkanin waɗanda suke takarar shugabancin jam’iyyar sun janye wa Abdullahi Adamu.
An yi ta kai ruwa rana dai kafin gamsar da ‘yan takarar su amince su janye wa Abdullahi Adamu, wanda shi ne shugaba Buhari ke marawa baya.
Kafin lokacin dai dukkanin ‘yan takarar sun gudanar da zama tare da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, inda suka Buhari ya fito karara ya bayyana musu cewa shi Abdullahi adamu yake goyon baya, ya kuma tashi ya bar su nan a zaune shi kuma ya shige cikin gida, ya bar su da mai kula da ayyukan fadar shugaban kasa.
Wannan lamari dai ya so ya tayar da kura, a lokacin da sauran ‘yan talarar ke kallon abin da Buhari ya yi musu a matsayin tozarci ko cin fuska.
Daga karshe dai an daddale magana kuma an shawo kansu, inda suka janye suka bar wa wanda Buhari ke goyon baya domin kaucewa kara fadada barakar da ke a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.