Najeriya Jami’an Tsaro Sun Yi Dirar Mikiya Kan Wadanda Suka Shigo Da Gurbataccen Man Fetur.
Bisa umurnin da shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar na gudanar da bincike don gano yadda gurbataccen man fetur ya shigo kasar, a halin yanzu jami’an tsaro sun fara yiwa shuwagabannin manya-manyan kamfanonin man fitur na kasa da kuma wasu hukumomin da abin ya shafa. Wadanda suka hada da kamfanin NNPC, da Oando da wasu da dama.
Jaridar Leadership ta Najeriya ta ce wata majiya wacce bata son a fadi sunanta ta khabarta mata kan cewa shuwagabannin wasu manya-manyan kamfanonin man da abin ya shafa sun fara fadin rawan da suka taka wajen shigo da gurbataccen man fetur lita miliyon 100 kasar.
Labarin ya kara da cewa a lokacinda labarin shigo da gurbataccen man fetur ya watsu da farko an dakatar da darakatan hukumar (NMDPRA),Farouk Ahmed daga aikinsa kafin a kammala bincike.
Labarin ya kara da cewa a lokacinda labarin ya isa kunnen shugaban kasa ya bukaci karamin ministan man fetur Timipre Sylva da ya tambayi Faruk Ahmed yadda aka yi gurbataccen man fetur lita miliyon 100 suka shigo kasar. Wasu kamfanonin da abin ya shafa sun hada da Emadeb, Oando,Duke Oil da kuma MRS.