Najeriya; Jami’an Tsaro Sun Ce Sun Kashe Wani Adadi Na ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna.
Jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama a wani samame da suka kai a yankin Galbi da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce rundunar Operation Forest Sanity tare da haɗin gwiwar sojojin sama suka far wa matattarar ƴan bindiga a yankin na Galbi.
Duk da cewa kwamishinan bai bayyana adadin ƴan bindigan da aka kashe ba, amma ya ce dakarun sun samu nasarar ƙwace bindigogi masu sarrafa kan su guda biyu da kuma AK47 guda uku da babura bakwai.
READ MORE : Ra’isi: Iran Ba Zata Dogara Da Sakamakon Tattaunawar Nukiliya Ba.
Ya bayyana cewa tun da farko dakarun sun tsallaka Kogin Kaduna inda suka rinƙa musayar wuta da ƴan bindigan, bayan haka ne suka samu kashe da dama daga cikinsu.
READ MORE : New York: Jami’an Tsaro Sunce Sun Tantance Makashin Salman Rushdi.
READ MORE : Libya: An Samu Girgizar Kasa A Birnin Bengazi.
READ MORE : Nasarallah; Iran Ce Zuciyar Al-Ummar Musulmi Kuma Cibiyar Gwagwarmaya.
READ MORE : An Bukaci Gwamnatin Lebanon Ta Gaggauta Kammala Yerjeniyar Sayen Makamashi Daga Iran.