Najeriya INEC Ta Fiatar Da Jadawalin Manyan Zabubukan 2023.
Hukumar zabe mai zaman kan ta INEC, a Najeriya, ta fitar da jadawalin babban zaben kasar dake tafe, inda za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar Asabar 25 ga watan February 2023.
Hukumar ta ce za a gudanar da zaben ‘yan majalisun tarayya tare da na shugaban kasar.
Zaben gwamnoni kuwa da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana a ranar 11 ga watan Maris na badi din.
Wannan ya biyo bayan rattaba hannu kan sabon daftarin dokar zaben kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a ranar Juma’a, bayan shafe dogon lokaci na cece-kuce kanta.