Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, ministan yada labaran najeriya Lai Mohammed ya bayyana haka lokacin da yake ganawa wakilan kafofin yada labarai a Washington dake kasar Amurka.
Ministan yada labaran na najeriya yace kiraye kirayen da wasu mutane ke yin a hukunta tubabbun mayakan kungiyar maimakon yi musu afuwa ya sabawa matakan da kasashen duniya ke dauka na kawo karshen ayyukan ta’addanci.
Mohammed yace ya tattauna da shugabannin sojin Najeriya kafin ya bar kasar kuma sun shaida masa cewar matakan da suke dauka sun yi daidai da wadanda ake dauka a kasashen duniya akan sojojin da suka aje makaman su ta hanyar kula da su a matsayin firsinonin yaki.
Ministan yace dokokin duniya sun hana budewa irin wadannan fursinonin yakin wuta ko kuma hukunta su, kuma matakan da sojojin Najeriya ke dauka kenan akan mayakan boko haram da suka mika kansu ga hukumomin soji.
Mashigar Rafah dai ita ce babbar mashigar da ake shigar da kayayyakin bukatar rayuwa ga al’ummar yankin Zirin Gaza, wanda Falastinawa mazauna yankin zirin Gaza suke yin amfani da ita domin ci gaba da rayuwa.
Gwamnatin kasar Masar tana yin amfani da mashigar Rafah domin yin matsin lamba akan Falastinawa musamman ma kungiyoyin gwagwarmaya na yankin zirin Gaza, inda ta kan rufe wannan mashiga a duk lokacin da ta ga dama, domin yin matsin lamba a kansu domin su amince da wasu bukatu na Isra’ila ko kuma wasu kasashen na daban.