Najeriya; EMA Ta Bukaci Da A Gurfanar Da ‘Yan Siyasar Da Suka Ki Bayyana Kadarorinsu.
Kungiyar fararen hula ta kasa da kasa ‘Egalitarian Mission for Africa’ ta yi kira da a gurfanar da dukkanin ‘yan siyasar da suka gaza bayyana kadarorinsu da suka mallaka kamar yadda dokar da’ar ma’aikata ta Nijeriya ta tanadar.
Kungiyar ta yi zargin cewa, mafi yawan wadanda suke karya dokar ‘yan siyasa ne, don haka ne suka nemi shugaban kotun da’ar ma’aikata (CCT), Justice Danladi Umar, da ya gurfanar da irin wadannan masu karya dokar don hakan ya zama izina ga na baya.
Kungiyar ta kuma yi zargin cewa, ma’aikatan gwamnati da dama da wasu ‘yan siyasa ciki har da wadanda suke neman a zabe su sun kasa ayyana adadin kadarorin da suka mallaka a rayuwarsu.
Shugaban Majalisar Amintattu na kungiyar, Dr. Kayode Ajulo, ya ce, kungiyar tasu za ta yi aikin hadin guiwa da kotun da’ar ma’aikata domin tabbatar da ana bin dokar ayyana kadarori ga dukkanin rassa da sassan gwamnati.
Dan rajin kare hakkin bil-adam na kungiyar Mista Ajulo ya kuma ce, kungiyar za ta yi aiki da hukumomin da abun ya shafa domin tattaro jerin masu karya dokar, “Za mu wallafa sunayensu kuma a karshe mu gurfanar da su a gaban kotun da’ar ma’aikata,” in ji Ajulo.
Kungiyar ta kuma ce, aiki ne na hadin gwiwa ga kowani dan kasa da ya ba da tasa gudunmawar wajen tabbatar da ana bin ka’idoji domin tabbatar da mulki na kwarai da gina kasa mai cike da adalci.
Ya kuma shawarci masu rike da mukaman siyasa da masu son a zabe su da su rika bin dokar da aka tanadar yana mai cewa babu yadda za su iya gudanar da wakilci na kwarai ba tare da suna bin doka ba.
Kungiyar dai ta bayyana fatan wadanda abin ya shafa za su dauki kiran da ta yi da muhimmanci.