Najeriya; Cinikin Man Fetur Na Gwargwadon Yadda Za’a Shigo Da Bukatar Cikin Gida.
Ministan kudi a tarayyar Najeriya Zainab Ahmed ta fadawa taron tattalin arziki na Davos kan cewa yawan danyen man fetur da kasar take sayarwa a halin yanzu bai fi na shigo da tattace don amfanin cikin gida ba.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Ahmed tana fadar haka a taron tattalin arziki na Davos da akakammala a kasar Swizlanda a makon da ya gabat.
Ahmed ta kara da cewa Najeriya bata samun kudaden da ta yi kasafinsa a rubu’ii na farko na wannan shekara. Ta kumakara da cewa matsalolin da kasar take mafa da su sun hada da satar danyen man fetur a yankunan da ake hakarsu da kuma masu lalata kayakan aikin hakar man a kudancin kasar.
READ MORE : Iran; Girgizan Kasa Mai Karfin Ma’aunin Richter 4.4 Ta Aukawa Yankin Qasre-Shirin.
A halin yanzu dai Najeriya tana hakar gangan miliyon 1.5 ne kacal., amma kuma ta yi kasafin kudinta na wannan shekara kan zata saida ganga miliyon 1.8 ne.
READ MORE : Bachelet – Musulmai A Yankin Xinjiang Na Rayuwa Daban Da Ta Mutane.
READ MORE : APC Ta Sauya Lokacin Zaben Fitar Da Gwanin Takarar Shugaban Kasa.