Najeriya; Atiku Abubakar Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Jam’iyar PDP.
Ajiya ne Babbar jami’iyar adawa ta PDP a najeriya ta gudanar da zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa a manyan zabukan da za’a yi a badi, inda Alh Atiku Abubakar tsohon shugaban kasar Najeriya ya lashe zaben bayan da kayar da sauran abokan hammaya , inda ya samu kuri’u 371,
Gwamanin Jihar rivers Nyesom Wike shi ne ya zo na biyu da kuri’u 237, sai dai tun kafin fara zaben gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da janyewa daga takarar ya barwa Atiku, kuma ya bukaci dukkan magoya bayansa da su zabi Atiku.
Tsohon shuagan majalisar dokoki na Najeriya Bokola saraki shi ne ya zo na 3 da kuri’u 70 sai kuma Udom Emanuel ya samu Kuri’u 38 , sai kuma kauran Bauci Bala Mohammad ya tsira da Kuri’u 20.
READ MORE : Najeriya; Cinikin Man Fetur Na Gwargwadon Yadda Za’a Shigo Da Bukatar Cikin Gida.
Yanzu haka dai dan takarar shugaban kasar na Jam’iyar PDP maishekaru 75 zai kara da dan takarar da Jam’iyya mai Mulki APC za ta fitar a zaben fidda gwani da za ta yi a ranakun 6 da kuma 7 ga watan yuni mai kamawa.