Najeriya;’ ASUU Ta Gindaya Wa Gwamnatin Tarayya Sharudda Kafin Ta Janye Yakin Aiki.
Kungiyar malamai masu koyarwa ta jami’o’i, ASUU, ta kalubalanci gwamnatin tarayya da ta karba tsarin biyan albashi na University Transparency and Accountability, UTAS, domin ta janye yajin aikin da ta tsunduma.
Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya sanar da hakan yayin zantawa da gidan talabijin na Channels a daren Litinin, yace zasu cigaba da yajin aikin har sai gwamnati ta karba UTAS kuma ta karrama yarjejeniyar su ta 2009.
ASUU ta shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 wanda a ranar Litinin din nan ne ta cika kwanaki 140
Bukatun dake cikin yarjejeniyar sun hada da cewa za a dinga jin halin da aikin Malaman jami’o’in ke ciki duk shekara biyar, matsalar albashi da alawus, gyaran jami’o’in da sauransu. A yanzu akwai matsalar UTAS da kuma rashin daidaito na IPPIS.
A ranar Laraba da ta gabata, Chris Ngige, ministan kwadago da aikin yi, yace gwamnatin tarayya nan babu dadewa za ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta tsunduma watanni hudu da suka gabata.
Ya kara da cewa, matsalolin bangaren biyan albashi da salon da gwamnatin tarayya ta zo da shi wanda kungiyar bata aminta da shi ba duk za a shawo kan shi a taron da za ta yi da kungiyar a ranar Alhamis.