Najeriya; APC Ta Shiga Wata Sabuwar Dambarwa Kan Batun Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa.
A zaman da kwamitin gudaarwa na APC ya gudanara jiya, shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da cewa sun yanke shawarar tsayar da shugaban majalisar Dattawa Ahamad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan ganawar da ya yi da shugaba Buhari a kebe, sai dai bayan sanarwar da ya bayar, gwamnonin arewacin Najeriya da ke goyon bayan a bayar da takarar jam’iyyar ga dan kudancin kasar sun yi watsi da sanarwar, yayin da kuma wasu daga cikin ammbobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC suka ce ba da yawunsu aka fitar da wannan sanarwa ba.
Wannan lamari ya jefa jam’iyyar cikin wani hali mawuyaci, ta yadda ba ta san alkiblar da ta dosa ba.
Sakamakon fusata da shugaban jam’iyyar ta APC Abdullahi Aamu ya yin ea lokacin da ake cikin tayar da jijiyar wuya bayan sanarwar tasa, sai ya kori dukkanin ‘yan jarida da ke daukar rahotanni daga ofishin jam’iyyar.
A daidai lokacin da wasu daga cikin jiga-jigar jam’iyyar ke cewa sanarwar da Abdullai Adamu ya bayar tana nuni ne da matsayin shugaban Buhari, domin ya bayar da sanarwar ne bayan ganawa da Buhari, wasu kuma daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar na cewa Buhari bai fito fili ya furta da bakinsa cewa ga wanda yake goyon baya ba, illa dai kawai yana cewa da ‘yan takarar su sulhunta su yi maslaha.