Najeriya; An Kasa Samun Daidaito Tsakanin Gwanoni PDP Kan Batun Karba-Karba.
Gwamnonin da suka fito daga shiyar kudancin Najeriya a karkashin Jam’iyyar PDP sun ce ba zasu taba yarda da shirin watsi da karba karba a cikin jam’iyyar ta su ba, lura da cewar wasu jiga jigan PDP na yunkurin ganin an bude kofar takarar shugabancin kasar na shekara mai zuwa domin baiwa jama’a daga kowanne bangare damar tsayawa.
Bayan wani taro da suka gudanar a Abuja, gwamnonin sun bayyana cewar sun fahimci ana shirin yaudarar su wajen hana su damar fidda dan takara daga kudancin kasar kamar yadda akayi alkawari a zaben shekarar 2019 lokacin da Jam’iyyar PDP ta gabatar da ‘dan arewa.
Ta bakin Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, Gwamnonin sun bayyana karara cewar suna goyan bayan hadin kan Najeriya da kuma jam’iyyar ta su wadda suka yi iya bakin kokarin su wajen ganin ta ci gaba da dorewa domin ceto Najeriya a shekarar 2023.
Sai dai sun ce kamar yadda suka bayyana a taron da suka yi a Lagos da Delta, ya zama wajibi Jam’iyyar ta mutunta shirin karba karba wajen tsayar da ‘dan takara daga kudancin Najeriya a zaben shekara mai zuwa.
Gwamnonin sun ce basu ga dalilin da zai sa su sauya ra’ayin su ba, saboda haka suna dakon jam’iyyar su ta PDP wadda aka kafa ta akan gaskiya da adalci ta mutunta alkawarin da tayi.
Yanzu haka masu sha’awar tsayawa takarar shugabancin Najeriyar a PDP sun fito daga arewaci da kudancin Najeriya, yayin da wata tawagar ‘Yan takarar a karkashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ke ziyarar jihohin kasar domin janyo hankali ‘yayan jam’iyyar wajen amincewa da bude takarar ga kasa baki daya maimakon baiwa yankin kudancin kasar.
Daga cikin wadanda suka nuna sha’awar takarar zaben daga arewacin Najeriya akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na Bauchi Sanata Bala Muhammed da Muhammad Hayatudden.