Najeriya; An Kai Wa Ayarin Motocin Tawagar Buhari Farmaki A Katsin.
Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin motocin tawagar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari hari a cikin jihar Katsina.
Mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ne ya sanar da hakan, inda ya tabbatar da cewa an yi wa ayarin motocin tawagar kwantan bauna, kuma an bude musu wuta a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsian.
Garba Shehu ya bayyana cewa shugaba Buhari baya a cikin tawagar, sai dai masu yi masa hidima da wasu daga cikin jami’an tsaro, da suka hada da masu tsaron lafiyarsa, da sojoji da ‘yan sanda gami da jami’an hukumar tsaro da DSS, amma babu wanda ya rasa ransa, sai wasu mutane biyu daga cikin tawagar sun samu raunuka, kuma tuni aka garzaya da su asibiti.
Sanarwar ta kara da cewa, lamarin ya faru ne a lokacin tawagar ke kan hanyarta ta zuwa Daura domin yin shirye-shirye kafin isowar shugaba Buhari, inda zai yi bukukuwan salla babba a garin na Daura.
Jihar Katsina wadda ita ce jihar shugaba Buhari, na daga cikin jihohin da matsalolin tsaro suka yi kamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman matsalolin satar jama’a domin karbar kudin fansa da ya zama ruwan dare a wasu yankunan kasar.