Wani bidiyo da ake cewa na sabbin takardun Naira 2000 da N5000 suna ta zagaye soshiyal midiya.
A takardun kudin an rubuta babban bankin Najeriya tare da hotunan fitattun ‘yan Najeriya da aka saka.
A ranar Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin takardun Naira a taron majalisar zartarwa.
Wani bidiyo dake yawo a soshiyal midiya ballantana Twitter, ya bayyana sabbin takardun kudaden Najeriya da suka hada N5000 da N2000.
Bidiyon wanda ya bayyana muryar wata budurwa yace sabbin kudaden Naira ne da za a fitar ranar 15 ga watan Disamban 2022.
Binciken Legit.ng Sai dai binciken da Legit.ng tayi ya bayyana bidiyon da ya yadu yana nuna sabbin takardun kudin tsoho ne kuma ya sake fitowa ne bayan an bayyana shirin sauya takardun Naira.
Bidiyon dake yaduwa a soshiyal midiya ya karade ne tun 2020 kusan shekaru uku da suka gabata.
Muryar budurwa na cewa: “Wannan mutumin ya zo nan a yau domin zuba kudin a asusun bankinsa na wannan reshen. Kuma yayi ikirarin cewa shi mahaukaci ne.
Yace N18 miliyan ne amma bayan mun kirga muka ga N17 miliyan ne.”
Me yasa bidiyon ya sake fitowa?
Babban bankin Najeriya a cikin kwanakin nan ya bayyana cewa za a sake fasalin wasu takardun Naira da suka hada da N100, N200, N500 da N1000.
Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele, wanda ya sanar da wannan shirin a taron manema labarai a ranar Laraba, yace sabbin kudaden zasu fara yawo a ranar 15 ga watan Disamban 2022.
Duk da Emefiele bai kara da cewa bankin zai gabatar da karin wasu takardun kudi ba, an fara yada cewa za a yi takardun N2000 da N5000.
Za ta share talauci ne? Frashin tsintsiya 1 a N11,200 ya sa jama’a sun girgiza a intanet.
A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto muku cewa Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa za a sauya fasalin takardun Naira ne saboda boye ta da ake yi.
An gano cewa, sama da kashi 80 na kudin Najeriya baya ma’adanar bankunan ‘yan kasuwa, duk suna boye ne, hakan kuwa babbar nakasa ce ga tattalin arzikin Najeriya.
Gwamnan bankin ya sanar da cewa, daga ranar 31 ga watan Janairun sabuwar shekara, duk wanda yake rike da tsofaffin takardun kudi bai kai an canza masa ba tamkar rike yake da takardar tsir.
Source:Legithausa