Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON), ta bayyana cewa Nijeriya ba za ta yi amfani da sararin samaniyar kasar Sudan ba, wajen jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin bana.
Shugaban NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ne, ya bayyana hakan a yau a wani shiri na gidan rediyon Freedom da ke Kaduna.
Malam Jalal Arabi ya tabbatar da Nijeriya ba za ta yi amfani da sararin samaniyar Sudan a lokacin tashin jiragen maniyyata saboda tsaro.
Don haka ya ce jiragen saman guda uku da aka bai wa kwangilar jigilar maniyyata da suka hada da MaxAir da Peace Air da kuma Flynas sun shirya tsaf domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Ya kuma bayyana cewa a ranar 15 ga watan Mayu ne, za a fara jigilar maniyyatan Nijeriya daga jihar Kebbi zuwa kasa mai tsarki a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.
Arabi, ya kuma bayyana cewa ana sa ran tawagar farko ta ma’aikatan NAHCON da suka hada da likitoci da ‘yan jarida za su tashi zuwa kasa mai tsarki nan da kwanaki masu zuwa domin shirya tarbar maniyyata.
A wani labarin na daban gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA), domin gina sakatariyarta reshen jihar a Binrin Kebbi.
Ya bayar da wannan gudummawar ne a lokacin kaddamar da kwamitin gyaran fuska na shari’a, kwamitin gudanarwa da kuma kaddamar da wasu karin sassa biyu a ma’aikatar shari’a ta jihar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta samar wa alkalai da lauyoyi hanyoyin sufurin da suka dace, yana mai cewa ya samar da kudaden da za a gyara ababen hawansu.
“Ina girmama bangaren shari’a, kuma na kuduri aniyar kawo sauyi a bangaren domin a gaggauta gudanar da ayyukan adalci da kuma samun adalci ga kowa, ba tare da tsangwama ba.
DUBA NAN: Kwamitin Wucin Gadi Ya Fara Bincikar Gwamnatin El- Rufa’i A Kaduna
Gwamnan ya yabawa majalisar dokokin jihar bisa gaggarumar amincewa da kudurin dokar sake fasalin shari’a tare da bayar da gudunmuwar kawo sauyi a fannin shari’a a jihar.