Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi, ta wallafa hotuna da bidiyon dalleliyar sabuwar motar ta ta N30 miliyan.
Babu shakka mota ta dauka hankalin jama’a ganin cewa ba kowa ke iya taka irin ta ba sai hamshakai da wane-wane.
An ga jarumar cikin shigar riga da wando inda ta fizgo motar kirar Chevrolet Equinox ta 2019 wacce darajarta ta kai N30m kiyasin Labaran Kannywood.
Wasu sabbin bidiyo da hotuna na jaruma Nafisat Abdullahi tana shagalinta da tsadajjiyar mota ya dauka hankulan jama’a masu tarin yawa.
Ba kuwa komai bane ya dauka hankalin jama’a ba illa zukekiyar mota da aka ga jarumar ta fizgo wacce ta kasance ‘yar yayi wacce ba kowa ke iya hawanta ba sai wane da wane ke iya hawan irinsu.
Bayyanar bidiyo da hotunan motar jaruma Nafisa Abdullahi ta N30m ta dauka hankali.
“Tauraruwa Nafisat Abdullahi tana ratuwar jin dadi da kece-raini inda a yanzu haka take tuka tsadaddiyar motar ta kirar Chevrolet Equinox LS ta 2019 mai darajar sama da Naira miliyan 30.”
A wani labari na daban, kamar yadda Legit.ng ta gano, batun da yafi yi wa ‘yan Kannywood zafi a maganar sarkin waka shi ne batun lalata da mata kafin a saka su a fim inda matan Kannywood ke ta fitowa suna musanta waccan maganar da yayi.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta rubuta budaddiyar wasika cikin harshen turanci a shafinta na Instagram kuma ta kara da bayani a kasan wasikar da harshen Hausa inda ta bayyana cewa babban zargi ya fitar tunda ta na cikin matan masana’antar.
Jarumar ta yi kira ga sarkin wakan idan ya na da matsala da wani ne, ya bayyana sunansa su yi ta kare ba wai ya bata masana’antar ba baki daya.
Har ila yau, a zancenta cikin budaddiyar wasikar, ta yi kira ga matan masana’antar kan cewa duk wacce darakta ko furodusa ya taba nemanta da lalata, ta fito ta bayyana sunansa domin a magance matsalar.
SOURCE:legithausang